Matar shugaban Najeriya Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta nemi afuwar ‘ya’yanta da iyalanta da kuma daukacin ‘yan Najeriya kan duk wani abin kunya da bidiyon da aka gan ta tana fada a ciki ya jawo, wanda ya yadu kamar ruwan dare a makon da ya gabata.
A cikin bidiyon dai an ji Aisha Buharin tana ta bambamin fada a harshen Turanci, duk da dai ba a nuna fuskarta ba.
A ranar da ta dawo daga Ingila ta tabbatar da cewa ita ce a bidiyon amma diyar Mamman Daura Fatima ce ta dauke ta. Fatiman dai ba ta musanta ba a lokacin da BBC ta tuntube ta.
Ta nemi afuwar ne a ranar Laraba lokacin da ta karbi bakuncin matan gwamnonin kasar 36 a fadar shugaban kasar, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka mata kan yada labarai Suleiman Haruna ya fitar.
Haka kuma ta wallafa sakon ban hakurin a shafinta na Instagram.
Tsallake Instagram wallafa daga aishambuhariKarshen Instagram wallafa daga aishambuhari
Ga bin da sakon ke cewa:
“Na yi farin cikin wanan ziyara da matan gwamnoni da matar shugaban majalisar dattawa da ta majalisar dokoki da matan ‘yan majalisar suka kawo min don yi min barka da dawowa.
Ina so na yi amfani da wannan damar wajen jinjina musu kan aiki na gari da suke yi a jihohinsu tare da hadin gwiwar shirina na Future Assured.
“Ina kuma ba su shawara da kar su bari wani abu da ake yadawa a kafafen sada zumunta ya dauke musu hankali ko wani abu daban na kafafen sadarwa.
“Ina amfani da wannan damar don neman afuwa kan abin kunyar da watakila na jawowa ‘ya’yana da iyalaina da dangina da ma ‘yan Najeriya baki daya da kuma kujerar da nake wakilta kan bidiyon da ya bulla wanda ya yadu tamkar wutar daji.
“Gaba dai gaba dai Najeriya.”
A wata daban kuma Aisha Buharin godiyarta ta mika zuwa ga maigidanta shugaban Najeriya kan sabbin mukamai shida da ya yi wa ofishinta na masu taimaka mata na musamman.
Hakan na kunshe ne duk cikin sanarwar da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya fitar a ranar Larabar.
Mutanen sun hada da:
Dr. Mairo Almakura – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka AFLPM.
Muhammed Albishir – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka kan Ci gaba OAFLAD.
Wole Aboderin – Mai taimaka mata na musamman kan Kungiyoyi MAsu Zaman Kansu NGOsBarista Aliyu Abdullah – Mai taimaka mata na musamman kan Harkokin YAda LabaraiZainab Kazeem – Mai taimaka mata ta musamman kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi
Funke Adesiyan – Mai mataimaka mata kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi.
Dama dai tun kafin a fitar da wannan sanarwa, an ji Aisha a hirar da ta yi da manema labarai ranar dawowarta tana cewa ta godewa mijinta Shugaba Buhari kan bayar da sabbin mukamai har shida na ofishinta.
Matan gwamnoni sun yi mata maraba
Matar gwamnan Bornon Hajiya Falmata Zulum ce ta jagoranci matan gwamnonin arewacin Najeriya yayin da matar gwamnan Edo Betsy Godwin Obaseki ta jagoranci matan gwamnoni daga kudu.
Hajiya Falmata ta ce sun je fadar shugaban ne don yi wa Aisha Buhari maraba bayan da ta shafe tsawon lokaci ba ta kasar, dannan kuma su kara tabbatar da goyon bayansu kan ayyukanta.
Sauran matan da suka halarci taron sun hada da matar mataimakin shugaban Najeriya Dolapo Yemi Osinbajo da Maryam Ahmad Lawan matar shugaban majalisar dattawa da kuma Salamatu Femi Gbajabiamila.
A nata bangaren uwargidan shugaban kasar ta sha alwashin gina sakatariyar yanki ta Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka AFLPM.
A shekarar 1995 ne aka kirkiri AFLPM a babban taron Beijing na kasar China.