Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya tabbatar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da takardar kudin Naira a gobe Laraba 23 ga watan Nuwamba, shekarar 2022. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Emefiele ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin kudi na babban bankin kasa na wata-wata a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kebbi: FG Ta Amince Da Naira Billiyan 32 Domin Aikin Hanyar Jega Zuwa Aleiro
Idan za a iya tunawa cewa, Dimokuradiyya ta nalkato a watan Oktoba Emefiele ya bayyana cewa, babban bankin zai fitar da sabon takardun kudi na Naira 200, Naira 500, da Naira 1,000, daga ranar 15 ga Disamba, 2022.
Sai dai, ya bayyana cewa CBN ba zai jira har zuwa watan na Disamba ba don bayyana sabbin takardun kudin da aka yiwa kwaskwarima.
Ya ce ba za a sauya wa’adin dawo da tsofaffin takardun kudin Naira zuwa bankunan kasuwanci ba don musanya su da sabbin kudaden.
A wani labarin kuma, Napoli Ta Zayyana Yan wasa Biyar, Da Za Su Iya Maye Gurbin Osimhen
Kungiyar Kwallaon kafa ta Napoli dake gasar Seria A ta kasar Italiya ta fitar da ‘yan wasa biyar da za su iya maye gurbin dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
An ruwaito wasu manyan kungiyoyin Turai na zawarcin Osimhen biyo bayan irin gudun mawar dake bai wa kungiyar.