Babban bankin Najeriya, CBN, Gwamna Godwin Emefiele, a ranar Talata ya dage kan cewa ba za a sauya wa’adin dena amfani da tsoffin takardun kudi na Naira ba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Emefiele ya jaddada cewa, wa’adin zai kare ne a ranar 31 ga watan Junairu, 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobe Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Takardun Kudin Naira – Emefiele
“A’a, ba za mu canja wani wa’adi ba, abin da muka yi bai saba wa doka ba; yana da alaƙa da doka.
“Mun sanar da wannan shirin ne a ranar 26 ga Oktoba, 2022, kuma mun ce bayan fitar da sabon kudin, matsayin amsan kudin a tsarin siye da siyarwa zai kare ne da tsohon kudin a ranar 31 ga watan Janairu 2023.
“Kusan kwanaki dari 100 ne, kwana 100 ya isa kowane mutum a kowane yanki na Najeriya ya ajiye kudinsa a banki sannan ya shirya ya cire kudi idan aka fitar da sabbin takardun kudi,” in ji gwamnan babban bankin.
A wani labatin kuma, Kebbi: FG Ta Amince Da Naira Billiyan 32 Domin Aikin Hanyar Jega Zuwa Aleiro
Gwamamnatin tarraya ta amince da fitar da zunzurutun kudaɗe da suka kai Naira biliyan talatin da biyu domin gina titin Jega zuwa Alerio da ke nan jihar Kebbi wanda tsawon nisan shi ya kai Kilomita 47.5.
Da yake jawabi a wurin ƙaddamar aiki wanda ya gudana a ƙarshen mako a garin Jega da Alerio, babban jami’in ofishin ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarraya da ke nan Birnin Kebbi Injinaya James K.Bugu yace kwangilar aikin zata ɗauki tsawon wattanin 24 inda aikin ake sa ran zai laƙume biliyan Naira 32