Granada ta kori kociyan kungiyar Robert Moreno bayan buga wasanni tara ba tare da samun nasara ba ya bar kungiyar a matsayi ta daya a saman teburin gasar La Liga.
Kungiyar ta fitar da takaitaccen bayani a ranar Lahadi inda ta ce ta yanke shawarar rabuwa da kocin ne a yammacin ranar Asabar bayan ta sha kashi da ci 3-1 a Valencia. kuma Wannan ne karo na shida da suka yi rashin nasara a wasanni bakwai na gasar.
Granada ta ci gaba da zama ta 17, maki uku sama da Alaves mai matsayi na 18.
Sanarwar ta ce “Kungiyar ta yanke shawarar a wannan Asabar don korar kocin kungiyar ta farko.” “Muna so mu gode wa Robert Moreno saboda aikinsa da sadaukarwarsa a wannan lokacin kuma muna yi masa fatan alheri a nan gaba.”
Kulob din ya kuma fuskanci wulakanci a gasar cin kofin Spaniya lokacin da Atletico Mancha Real mai mataki na hudu ta fitar da ita a watan Disamba.
Ruben Torrecilla, mai horar da ‘yan wasan ajiye, ya karbi ragamar kungiyar ta farko na wucin gadi.
Moreno, mai shekara 44, ya koma Granada a watan Yuni 2021 kan kwantiragin kakar wasanni biyu.