Daga karshe Gwamna Samuel Ortom ya kawo da rade-radin da ake ta yadawa game da burinsa na tsayawa takarar kujerar sanatan jihar Benue ta Arewa maso yamma, inda yanzu haka ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan a karshen mako.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, kujerar a halin yanzu tana hannun Sanata Emmanuel Orker Jev, wanda zai iya neman wa’adi na biyu domin ci gaba da wakilcin mazabarsa.
Ortom ya dai ya bayyana wannan aniya tasa ne tun a ranar Asabar, a lokacin da ya nemi albarkar ‘yan uwansa a wani taro da mutanen Nzorov da suka hada da sarakunan gargajiya da sauran shugabanni.
Gwamnan ya shaidawa ‘yan uwansa Nzorov cewa a yanzu ya gamsu da cewa zai tsaya takarar kujerar majalisar dattawa ta Zone B a karkashin jam’iyyar (PDP).
Da yake mayar da martani, Hakimin Nzorov, Cif Gwatse Akaahena, wanda ya yi magana a madadin shugabannin gargajiya da na siyasa sun ba da goyon bayansu ga gwamnan ya ci gaba da neman kujerar majalisar dattawa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Nathaniel Ikyur, ya sanyawa hannu, ta ruwaito basaraken na cewa su ‘yan uwansa suna goyon bayan dan su ba wai kawai ya tsaya takarar kujerar majalisar dattijai ba har ma ya mallaki manyan mukamai a kasar.
Tun da farko dai Ortom ya yi wa ‘yan uwansa jawabi a takaice, inda ya shaida musu cewa a karshe ya gamsu cewa Allah ya tabbatar masa da cewa zai tsaya takara kuma ya bukaci idan sun amince da wannan manufa.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Nzorov na jam’iyyar PDP, Ezekiel Adikpe, ya yi magana a madadin jam’iyyar daga yankin kansilolin gwamna.
Comments 1