Tsohon ɗan wasan gaba na Manchester United Mason Greenwood ka-iya komawa ƙungiyar daga sabuwar ƙungiyarsa ta Getafe.
Ƙungiyar ta Laliga ta ɗauki dan kasar Ingilar ne a matsayin aro bayan da United ta ce kwata kwata ba ya cikin tsarinta a yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Karewar Wa’adi: Dalilin da Yasa Na Bar Chelsea Zuwa Nottingham Forest — Hudson-odoi
Yanzu haka Greenwood zai shafe kakar bana a Spaniya inda a karshen kakar ne ake sa ran zai sake haɗewa da tsohuwar zumar tasa.
Rabon da Greenwood ya fafata wasa tun watan Janairun 2022 bayan da aka yi ram da shi bisa zargin cin zarafi budurwarsa.
Sai dai yanzu haka ɗan wasan zai fara sabuwar rayuwa a gasar Laliga inda ake kyautata zaton a watan Yunin baɗi zai sake komawa Old Trafford.
“Akwai yiwuwar Greenwood zai sake haɗewa da Manchester United a watan Yunin 2024 bayan da ya bar ķungiyar zuwa Getafe a matsayin aro.
“Manchester United ita ta biyan rabin albashin Greenwood yayin da Getafe za ta rika biyan rabi, kamar yadda shahararren dan jaridar wasanni Fabrizio Romano ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.
Gabannin haɗewar Greenwood da Getafe dai an sha alaƙanta shi da manyan ƙungiyoyi ciki har da Arsenal da Real Madrid da kuma Inter Milan.