Dalibai mata da aka ceto na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUG), sun samu tallafin kudi daga Gwamnatin Tarayya domin rage masu wahalar da suka sha a hannun barayin daji.
Kwamishinan Agaji na Zamfara, Alhaji Salisu Musa ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar Malam Bashir Kabir a Gusau ranar Talata.
Ya ce an bayar da tallafin ga wadanda abin ya shafa ta hannun ma’aikatar kula da jin kai da yaki da fatara ta tarayya.
Karanta nan‘Yan Sanda Sun Kama Wadda Ake Zargi Da Kisan Malamar Jami’a A Minna
Kowace daga cikin daliban 14 ta samu kyautar kudi Naira N214,285 tsabar kudi daga gwamnatin tarayya.
A madadin gwamnatin Zamfara, muna godiya da wannan karimcin da kuma ministar gwamnati Dr Betta Edu, saboda irin taimakon da daliban suke yi,” in ji shi.
Ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na hada kai da gwamnatin tarayya wajen ceto mutanen da bala’in ya shafa a jihar.
Kwamishinan ya yabawa mahukuntan jami’ar da iyayen wadanda abin ya shafa saboda hakuri da fahimtar juna da goyon baya da hadin kai a wannan lokacin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ministan ya kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar inda ya jajantawa jami’ar da wadanda abin ya shafa.
A wani labarin Kuma
Zamu Mayar Da Hankali Akan Sauran Albarkatun Kasa Wadanda Ba Man Fetur Ba-Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na mayar da hankali wajen tono sauran arzikin kasa da Allah ya albarkaci kasar da su a maimakon cigaba da dogaro da man fetur da kasar ke hakowa.
Gwamnatin ta bayyana cewar zata mayar da hankali wajen tono sauran abubuwa kamar Silver,Gwal,Kwal da sauran albarkatu domin ragewa man fetur nauyin da aka dora masa.