Mutane 69 ne har yanzu ba a kai ga ganowa ba tun bayan wani kwale-kwale da ke jigilar mutane sama da 100 a gabar kogin Benue ya kife a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Jaridar Vanguard a ranar Lahadi ta ruwaito cewa jirgin na kan hanyar zuwa garin Binnari ne daga kasuwar kifi ta Mayorenewo lokacin da lamarin ya faru.
Karanta nanGusau-Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Daliban Da Suka Kubuto Naira 200,000 Kowace
A wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta wallafa a shafukanta na sada zumunta daban-daban, fasinjoji 104 da suka hada da maza 42, mata 45 da kananan yara 17 na cikin jirgin.
A cewar NEMA, an fara aikin bincike da ceto, kuma daga cikin fasinjoji 104, an ceto mutane goma sha hudu (14), gawarwaki ashirin da daya (21) da aka gano yayin da mutum sittin da tara (69) suka bace.
An dakatar da ayyukan bincike da ceto yayin da muka cimma yarjejeniya da masu ruwa da tsaki na cikin gida don ci gaba da lalube.
Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Alhaji Aminu Abdullahi Alkali tare da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata, 31 ga Oktoba, 2023 sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.
Inda yayi kira ga daukacin al’ummar wurin da su tabbatar da amfani da rigunan ceton rai a duk lokacin da zasu yi tafiya a jrigin ruwan mai fadi da kuma zurfi.
A wani labarin kumaTsohon Shugaban Jam’iyar NNPP Rufai Alkali Ya Koma APC Tareda Magoya Bayansa
Matsalar kifewar kwale kwale a Nijeriya ba sabon abu bane,inda an sha samun rahotannin kifewar jirgin kwale kwale a lokuta da dama.
A wasu yankuna na Birnin Yauri dake jahar Kebbi da kuma wasu yankuna na yammacin jahar Neja dake Arewa ta tsakiyar Nijeriya.