Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya baiwa jami’an tsaro aikin tabbatar da cikakken kariya da mutunta muhimman hakkokin ‘yan kasa a jihar.
Yusuf ya bayyana haka ne ta bakin babban daraktan ayyuka na musamman na gidan gwamnati, AVM Ibrahim Umar mai ritaya, a wajen wani taron horaswa na kwana daya da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shirya.
Karanta nanDa Dumi-Dumi: Tinubu Ya Bada Tabbacin Za A Yi Kidayar ‘Yan Najeriya Nan Bada Dadewa Ba
Gwamnan ya bukaci jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar da ke halartar taron karawa juna sani da ‘nitty gritty’ na hukumar kula da tsarin shari’a ta kasa (ACJL) ta shirya da su mutunta hakkin dan adam yayin gudanar da aikinsu.
A cewarsa, taron horaswar karo na biyu ya nuna wani gagarumin ci gaba wajen inganta kwarewar jami’an tsaro don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata tare da bin dokokin shari’ar laifuka a jihar.
Yusuf ya ce taron na nufin wani gagarumin ci gaba a yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da adalci.
Yusuf ya ci gaba da cewa ACJL ta kasance muhimmiyar doka da ke neman daidaitawa da kuma zamanantar da tsarin shari’ar laifuka.
Gwamnan ya ce, “Yana bayar da muhimmanci sosai wajen kare hakkin wadanda ake tuhuma da wadanda aka kashe, tare da tabbatar da cewa an yi adalci a kan lokaci.
A wani labarin kumaTinubu Bai Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Suke Ciki Ba–Peter Obi
Gwamna Yusuf ya lura da cewa taron bitar ya zo ne a wani muhimmin lokaci lokacin da al’ummarmu ke fuskantar kalubale masu tasowa wadanda ke bukatar a bi tsarin gudanar da adalci.
ACJL wani muhimmin al’amari ne da ya samar mana da tsarin shari’a don tunkarar wadannan kalubale na tabbatar da adalci a jihar Kano inji shi.