Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya kafa dokar ta-baci saboda tabarbarewar tsaro a jihar, biyo bayan barkewar tarzoma na ‘yan daba a babban birnin jihar, Minna.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bikin Sallah da tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu ya shirya a gonarsa da ke Minna.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ka sauke duk wanda ka naɗa daya kasa taɓuka komai – El-Rufai ga Tinubu
Mista Bago ya kara da cewa, ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wani dan daba da aka samu yana barazana ga zaman lafiya a jihar.
Umarnin na gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ayyukan ‘yan daba suka sake kunno kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a daren Juma’a a Minna.
Mista Bago, wanda ya danganta sake barkewar rikicin da ayyukan masu hakar ma’adanai a babban birnin jihar, ya ce ya bayar da umarnin rufe dukkan wuraren hakar ma’adanai.
“Na ayyana dokar ta-baci kan harbin da aka gani kan duk wani dan damfara da aka samu a cikin babban birni da kuma cikin jihar.
“Ba mu da hakuri kan rashin tsaro da ‘yan daba. Mun kuma rufe wuraren da masu aikin hakar ma’adanai ke haddasa wannan barna a jihar.
“Duk wanda aka samu a wurin za a harbe shi har lahira. Wadanda ke daukar nauyin su ma za a yi musu hukunci mai tsauri,” in ji Mista Bago.
A wani labarin kuma:Shugaba Tinubu ya ayyana ranar 7 ga Afrilu a matsayin ranar ƴan sanda ta ƙasa
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sanda ta kasa.
Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana haka ne a daren ranar Litinin a yayin bikin karramawa da yabo na ‘yan sandan Najeriya da aka gudanar a Transcorp Hilton, Abuja.