Ka sauke duk wanda ka naɗa daya kasa taɓuka komai – El-Rufai ga Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke duk wanda ya nada wanda ya kasa cika aikin sa.
El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri a ranar Litinin, inda ya bukaci shugaban kasar da ya kuma duba yiwuwar gyara wasu manufofinsa da ba sa samar da sakamakon da ake bukata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda gwamnatin Najeriya ta ceto mutane sama da 1000 da aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba – NSA
“Kun nada mutum mukami kuma ba ya aiki yadda ake tsammani, ya kamata ku kasance da tawali’u don gaya masa cewa ina bukatan wanda ya fi haka, je ka yi wani abu,” in ji El-Rufai.
El-Rufai ya kuma yi kira da a yi addu’a da goyon bayan ’yan kasa ga gwamnati a yunkurinta na ganin ta dawo da al’amura yadda suka kamata.
“Abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na ’yan kasa shi ne mu yi wa shugabanninmu addu’a don Allah Ya yi musu jagora su gani ko su yi abin da ya dace.
“Domin Allah ya ba su tawali’u su juyar da kansu a lokacin da ya dace kuma su yi abin da ya dace; haka al’umma ke ci gaba,” in ji shi
A wani labarin kuma:Sai da muka aika da gargaɗi ga Isra’ila – Iran
Jami’an Turkiyya, Jordan da Iraki sun fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa Iran ta ba da sanarwar kwanaki kadan kafin harin da jiragenta mara matuki da makami mai linzami suka kai kan Isra’ila, amma jami’an Amurka sun ce Tehran ba ta gargadi Washington ba, kuma tana da niyyar yin barna sosai.
Iran ta harba daruruwan jirage marasa matuka da makamai masu linzami a ranar Asabar a wani harin ramuwar gayya bayan wani hari da ake zargin Isra’ila ta kai a harabar ofishin jakadancinta da ke Siriya.