Gwamna Buni ya ayyana hutun ranar Litinin domin murnar sabuwar shekarar Musulunci
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, 2022, a matsayin ranar hutu domin Ma’aikatan Gwamnati da sauran al’ummar Jihar damar gudanar da bikin Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1444 bayan Hijira.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Fiye Da Gwamnoni Biyar, Wasu Manyan Shugabannin Suke Aiki Ga Peter Obi — Jam’iyyar LP
Gwamnan, ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin Addini, Ustaz Babagana Malam Kyari ya taya Al’ummar Musulmi murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci tare da neman goyon bayan jama’a da haɗin kai domin Jihar ta samu daukaka da matsayi na cigaba.
Hakazalika Gwamna Buni ya buƙaci Al’ummar jihar da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya, da kuma samun Albarkar Noma a lokacin noman bana.
Haka zalika, za’a koma aiki ranar Talata, 2 ga Agusta, na Shekarar 2022, kamar yadda sanarwar ta bayyana.