Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ziyarci mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun a ranar Laraba, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Mamman Mohammed.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Shugabannin Kwadago Sun Sa Labule da Shugaba Tinubu a Villa
A cewar sanarwar, Gwamna Buni ya yi doguwar tattaunawa mai ma’ana kan bangarorin hadin gwiwa da ‘yan sandan Najeriya domin karfafa tsaro a fadin jihar.
Buni ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiyar da aka samu a jihar ba kawai ya dore ba har ma ya inganta.
“Wannan shi ne babban fifikon gwamnatinmu, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun cimma hakan, domin ganin jihar Yobe ta fi zaman lafiya ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki,” in ji Buni.
Mukaddashin IGP Egbetokun ya baiwa gwamna Buni da al’ummar jihar tabbacin shirin rundunar ‘yan sanda na kare jihar da al’ummarta.
Ya yabawa Gwamna Buni bisa wannan ziyarar da kuma kishinsa na tabbatar da tsaron jihar baki daya.
A wani labarin kuma, Zanga-zanga: NASS ta yi alkawarin magance bukatun NLC a cikin kwanaki 7
Majalisar kasa (NASS) ta yi alkawarin duba wa tare da magance bukatun da kungiyar kwadago ta gabatar a cikin mako guda mai zuwa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar kwadago ta gudanar da gagarumin zanga-zanga a harabar majalisar dokokin kasar inda ta gabatar da jerin bukatun ta ranar Laraba a Abuja.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC da TUC ne suka shirya wannan gagarumin zanga-zanga kan manufofin gwamnatin tarayya na yaki da talakawa da ma’aikata.
Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye da aka rubuta kamar haka; “Mun yi Allah wadai da karin kudin makaranta, “Dakatar da shigo da mai, a farfado da matatun mai,” “Karin farashin man fetur da ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki, talauci da sauransu.