Yanzu haka dai shugabannin kungiyoyin kwadago na Najeriya da suka hada NLC da TUC sun shiga ganawa da shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, kamar yadda Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Nijar: Burtaniya Na Goyon Bayan Yunkurin ECOWAS Na Maido Da Bazoum
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kungiyoyin suka gudanar da shirye-shiryensu na nuna rashin amincewarsu da halin kuncin tattalin arzikin da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
Idan dai za’a iya tunawa shugaba Tinubu ya bayyana kawo karshe tallafin na man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
A wani labarin kuma, Zanga-zanga: NASS ta yi alkawarin magance bukatun NLC a cikin kwanaki 7
Majalisar kasa (NASS) ta yi alkawarin duba wa tare da magance bukatun da kungiyar kwadago ta gabatar a cikin mako guda mai zuwa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar kwadago ta gudanar da gagarumin zanga-zanga a harabar majalisar dokokin kasar inda ta gabatar da jerin bukatun ta ranar Laraba a Abuja.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC da TUC ne suka shirya wannan gagarumin zanga-zanga kan manufofin gwamnatin tarayya na yaki da talakawa da ma’aikata.
Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye da aka rubuta kamar haka; “Mun yi Allah wadai da karin kudin makaranta, “Dakatar da shigo da mai, a farfado da matatun mai,” “Karin farashin man fetur da ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki, talauci da sauransu.
Akpabio wanda ya samu wakilcin, Ali Ndume, Babban Alkalin Majalisar Dattawa ya tabbatar wa ma’aikatan da suka yi zanga-zangar cewa NASS na goyon bayan gwagwarmayar su.