- Gwamna Elrufai ya sallami maaikata 99 ya Kuma bayyana cewa zai cigaba.
- Gwamnan Kasuna Nasiru Elrufai ya sallami maaikatan 99. Ya bayyana hakan ne ga manema labarai dake Kaduna.
- Gwamnan Nasirun ya bayyana sallamar maaikatan lokacin da yake ganawa da wadansu manema labarai a Kaduna, yake cewa kaso 30 cikin maaikatan duk yan alfarma ne.
Jaridar Dailytrust Yace “jahar tana bakin kokarinta wajan tabbatar da hakkokin jamaan amma haryanzu maaikatan basu gane ba”
Gwamnan yace yawancin maaikatan kananan hukumomi ne aka sallama Wanda ya hada kananan hukumomin 23 da kananan asibitoci.
Yace ” kawo yanzu dai maaikatan alfarma 99 suka rasa ayyukansu amma haryanzu babu maaikatan jaha da aka kora.
Ya cigaba da cewa “zamuyi iya bakin kokarinmu wajan yin adalci ga maaikatan jaha”
Ya Kara da cewa” tuni munyi alkawarin rage maaikatan sannan mun ce zamu fara da maaikatan alfarma ne Kuma munyi hakan.
Gwamnan yace lokacin da yake bayani a harshen Hausa korar maaikatan zai cigaba kamar yadda aka tsara saboda Karin haraji dake karuwa ma jahar daga asusun gwamnatin tarayya.
Yace kowane maaikaci dake da matsala da bayaninsa za’a bashi damar bayyana hujjojinsa kamin a zartar masa da hukunci.
Gwamnan yace kawo yanzu dai gwamnati sa ta baiwa mutane 11,000 aiki tun daga kan maaikatan Lafiya da Malaman Jami’a da Malaman Firamare da sakondari a fadin jahar.
A watan mayun shekarar 2021 ne albashin ma’aikatan alfarma ya kai kimanin miliyan 259, a inda ma’aikatan gaskiya albashin su baifi miliyan 3.13 ba.
Gwanman yace yayi alkawarin cigaba da biyan karancin albashi akan dubu 30,000 bazai daina ba.
Yace mune gwamnati na farko da muka fara biyan karancin albashi 30,000 wannan shiya ba ma’aikatan Karin albashin da kaso 66. Hakazalika bamu sauya yanayin biyan kudin Yan fansho ba akan naira dubu 30,000.
Yace gwamnati zatai iya bakin kokarinta na cigaba da biyan kudin fansho.
Comments 1