Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nemi ‘yan jihar da su yi amfani da wannan lokaci na bukin Kirsimeti wajen yin addu’ar samun hadin kai, zaman lafiya da kuma ci gaba a jihar baki daya.
Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na Kirsimeti da ya fitar a ranar Juma’a a garin Yola. Inda gwamnan ya taya al’ummar jihar musamman ma Kiristoci murnar wannan lokacin na bukin kirsimeti.