Rahotanni na nuni da cewa; akalla mutum 11 suka mutu cikin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai kan wani kauyen a jihar Borno wanda galibin mazauna kauyen Kiristoci.
Boko Haram din sun yi awon gaba da wani limamin Kirista da wasu mazauna kauyen Pemi a harin da suka kai a ranar Alhamis, inda suka ƙona gine-gine da wata coci.
Ganau sun ce maharan sun shiga garin na jihar Borno ne cikin motoci da babura suna harbin kan mai uwa da wabi a yayin da mutane ke shirye-shiryen shagulgulan Kirsimati.
Wasu mazauna garin sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukannsu.