Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da tambarin tashar tsandauri ta Dala wato {Dry Port da Kano Economic & Diaspora Investment Summit}.
An gudanar da taron ne a dakin taro na Legas, dake Otel din Transcorp Hilton, a birnin tarayya Abuja, wanda ya gudana yau Litinin.
Aikin wanda zai lakume biliyoyin Naira, wanda ke da nufin inganta tattalin arzikin jihar, gwamnatin Ganduje za ta fara aiwatar da shi kafin kashi na biyu na wannan shekara.
Wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo, Hon. Kwamishinan kasuwanci Barr. Ibrahim Muktar, Haji Hama Ali Aware, Alhaji Ahmad Rabiu da sauran wasu fitattun mutane.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, kakakin majalisar jiha, Right Hon Ibrahim Chdari, Alhaji Nasiru Aliko Koki, yan majalisar wakilai, kwamishinoni, SSA zuba jari na kasashen waje, Hon. Sani Ahmad Turaki da sauran jami’an gwamnati.