Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu a lokacin da suke aikin gonakinsu a unguwar Sardauna da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
An bayyana cewa an kashe manoman ne a ranar Lahadi da misalin karfe 3:30 na rana.
Shugaban ’yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad (Wanda akafi Sani da Blacky), ya bayyana sunan mamatan kamar haka; Hamza Na’allah da Zubairu Haruna da ke gundumar Sardauna a yankin Sabon Birni.
Blacky ya bayyana cewa su uku ne a lokacin da aka kai harin amma daya daga cikinsu ya tsere zuwa kauyen da ke kusa ba tare da wani rauni ba.
Ya ce duk da zaman lafiya da ake samu a yankin, har yanzu ana ci gaba da samun munanan hare-hare a cikin al’ummomin da ke nesa da cikin Garin Sokoto.
A cewarsa, ‘yan fashin sun yi garkuwa da mutane hudu a hanyar Sabon Birni zuwa Goronyo kwanaki hudu da suka gabata.
Sai dai an kasa samun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ta Wayar salula har zuwa lokacin hada wannan rahoto domin tabbatar da lamarin.