Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa sabon sakatare na din-din-din na ministirin kula ƙananan hukumomin jihar.
Gwamna Ganduje ya nada Yusuf Datti Hussaini, tsohon darektan albashi na ministirin, a matsayin sabon sakaraten din-din-din na ministirin kula da ƙananan hukumomi ta jihar Kano.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya na cakawa Ummita wuƙa -Ɗan Chana ga kotu
Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Abba Anwar, hadimin gwamna Ganduje ya fitar a ranar Alhamis 12 ga watan Janairun 2023.
Gwamnan yace kwazo da ƙwarewar Yusuf Datti sune suka sanya aka miƙa wannan sabon matsayin.
Tuni har antoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Barr. MA Lawan ya rantsar da shi domin fara gudanar da aikin sa.
Dimokuradiyya ta samo cewa manyan jami’an gwamnatin jihar da suka haɗa da mataimakin gwamnan jihar kuma ɗan takarar gwamnan jihar, Nasiru Gawuna da mataimakin sa Murtal Sule Garo, kwamishinoni da ƴan’uwa da abokan arziƙi suka samu halartar rantsuwar tasa.
Gwamna Ganduje ya buƙace sa da ya tabbatar a shirye yake a kowane lokaci domin yin amfani da sabbin hanyoyin zamani domin ganin ya ciyar da ministirin gaba.
“Duba da tarihin da kake da shi, ya nuna cewa kai mutum ne ƙwararre sannan ka cancanci samun wannan sabon matsayin a jihar nan. A yayin da kake ma’aikacin mai ƙima, muna roƙom ka da ka cigaba akan wannan turbar da kake a kai.” a cewar sanarwar.
Gwamna Ganduje ya umurci saban sakataren da yayi aiki tuƙuru cikin aminci tare da sauran ma’aikatan dake a ƙarƙashin sa. Inda ya tabbatar masa da cewa ana buƙatar haɗin kai a koda yaushe wajen tafiyar da ayyukan al’umma.
Yadda Aka Yiwa Wata Mata Fyaɗe a Gaban Ƴar Ta Mai Shekara 2
A wani labarin na daban kuma, wani ɓata gari ya shiga hannun hukuma bayan ya ketawa wata mata haddin ta.
Jami’an hukumar Nigeria Security and Civil Defense Corps (NSCDC) a jihar Ƙwara sun cafke wani wanda ake zargin da aikata laifin fyaɗe, mai suna Ganiyu Yusuf, mai shekara 47 a duniya.
Hukumar ta daɗe tana neman wanda ake zargin tun shekarar da ta gabata bayan an kawo rahoton aikata laifin fyaɗen.