Daga Mu’azzam Yakubu Sanka
Gwamnatin jihar Kano ta bada kwangilar gina bangaren kwantar da majinyata mai gadaje 52 a asibitin kwararru da akewa lakabi da Muhammadu Buhari wanda zai lashe kimanin Naira Miliyan 730.
Aikin, wanda zai kunshi dakuna da ofisoshin jami’an kiwon lafiyar Wato (Nurses) a Turance da Bangaren dafa abinci, makewayi da dai sauransu.
A yayin da ya kai ziyarar duba aikin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa an bada kwangilar yin aikin ne da nufin tabbatar da jin dadin majinyata musamman ma masu fama da ciwon daji (Cancer) daga fadin jihar da ma wasu jihohin.
Zamu samar da hanya tsakanin cibiyar lura da masu ciwon dajin da kuma sauran bangarorin majinyata a kokarin gwamnatin mu na samar da ingantaccen yanayin kiwon lafiya da zai zamo abin kwatance a fadin duniya”inji Gwamna Ganduje.
Dr. Ganduje yace za’a kammala aikin nan da wata 4 zuwa biyar masu zuwa sannan kuma za muyi aikin daga darajar asibitin wajen samar da kyakkyawan yanayin kiwon lafiya.
Nayi farin cikin jin labarin cewa wannan asibitin ya yi tiyatar kwakwalwa na farko wanda ake sa ran cewa kowanne asibitin gwamnatin jiha zai soma yi a wannan yankin na Najeriya.
Asibitin ya kuma gudanar da tiyatan jijiyar baya (spinal code surgery) ga wani majinyaci daya wanda wannan somawa ce, inji Ganduje.
Da yake magana akan cibiyar masu ciwon daji, Ganduje yace an bada kwangilar sa kuma yana mai cewa aikin zai soma a mako mai zuwa.
Gwamnan yace ya gano irin cibiyar jinyan masu ciwon daji a wata ziyarar sa da ya kai Kasar Australia.
Inda Ya kara da cewa don hakane Gwamnatin sa ta kwaikwayi irin cibiyar domin kawowa al’umar ta sauki ganin yadda masu ciwon ke karuwa a wannan lokacin wanda kuma Mafi yawan su bazasu iya biyan kudin jinyar ba.
Tuni ma har mun kawo wani kwararre daga kasar Italia, wanda zai sa ido akan aikin, Inji Gwamna Ganduje.