A yau ne nan gaba kadan ake saka ran cewa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai karbi fom dinsa, don tsayawa takarar sanatan Kano ta arewa.
Amincewar gwamnan na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da masu ruwa tsaki a jam’iyyar suka gudanar a gidan gwamnatin jiha, inda kuma ba tare da jayayya ba suka amince masa daya kasance dan takara a wannan shiyya.
Wata majiya mai tushe daga bangaren gwamnan ta ce ana saka ran yau litinin gwamnan zai karbi fom dinsa na tsayawa takarar, tare da bayyana sha’awarsa ga al’umma.
Idan har hakan ta tabbata to gwamna Ganduje zai gaje kujerar sanata mai ci a yanzu haka, wato sanata Barau Jibrin, wanda kuma tuni Barau din ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar nan.
Sanata Barau dai a baya yana daga cikin makusantan ganduje, wanda kuma ake kyautata zaton zai nuna shi a matsayin wanda zai goyawa takarar sa baya, amma daga bisani da aka samu wani rashin fahimta ya sanya sanata koma tsagin tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau.