Gwamna Jahar Katsina ya ɗauki nauyin Kiristoci 28 zuwa aikin ibadar su a kasar Isra’ila
Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta ɗauki nauyin Kiristoci zuwa aikin ibadar su ƴan asalin jihar Katsina kimanin su 28.
Kamar yadda Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta samu, kiristocin wadanda suka fitowa daga sassa daban daban na jihar za su je kasar Isra’ila ne da kasar Jordan domin ziyarar wuraren ibadar su da kuma wuraren tarihi masu muhimmanci a addinin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar siyawa Alkalai mota
Da yake karin haske a kan batun ga majiyar mu, mai baiwa Gwamna shawara akan addinin kiristocin, Rabaran Ishaya Jurau, ya bayyana cewa mutanen da gwamnatin ta dauki nauyi sun hada da jami’an gwamnati, malaman addinin kiristocin da kuma shugabannin su na majami’u daban-daban.
Rabaran Ishaya ya kuma kara da cewa wasu kiristocin su 28 daga jihar sun biya ma kan su kudin zuwan kuma da su za’a tafi.
Comments 1