Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisa ta 8 Shehu Sani ya bayyana mamaki na yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa wasu Ministoci a ƴan kwanakin nan.
Da yake jawabi a lokacin da aka tattauna dashi a cikin shirin Siyasar mu a Yau na gidan Talabijin na Channels a ranar Talata, Sani yace Buhari ya kamata ace ya sake naɗa Rotimi Amaechi tsohon Ministan Sufuri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Jahar Katsina ya ɗauki nauyin Kiristoci 28 zuwa aikin ibadar su a kasar Isra’ila
“Nayi mamaki dana karanta sunayen nan da aka turawa Majalisun Ƙasa. Yadda naga yayi tsaiko wajen naɗa Ministoci, da rashin matsaya akan wasu al’amura.
“Idan ka duba tarihi, kafin ya naɗa Ministoci, a lokacin da ya karɓi mulki a Shekarar 2015, ya ɗauke shi watanni, lokacin da akwai Minista daga Jahar Kogi daya mutu a dalilin hatsarin mota, sai da ta ɗauki lokaci kafin ya sake naɗa wani. Kuma akwai Ministocin noma da Makama shi. Ya ɗauke shi lokaci kafin ya naɗa wani.”
Sani ya bayyana cewar wannan shine lokaci na farko a tarihi da Ministoci a Ƙasar zasu wa’adi biyu a ofishin su a maƙami daya ba tare da canja su ba.