Gwamna Jihar Piltao Dakta Simon Bako Lalong ya ce babu abin da ya fi tsana a rayuwa kamar ganin ayyukan da ba a karasa ba a yashe, don dole ya yi duk mai yiwuwa don ganin ya karasa ayyuka da ya fara da ma wadanda ya gada gabannin ya bar ofis.
Lalong ya bayyana wannan matsaya tashi ne jim kadan bayan rangadi da ya kai guraben wasu ayyuka da yake gudanarwa a jihar.
Ya ce ko shakka babu almubazzaranci ne a ce gwamnati ta fara aiki amma ta gaza kammalawa sannan wacce ta gaje ta ma ta zo ta yi buris da shi.
“Mu a aniyar mu kamar yadda muka fadi, idan mun ga ayyuka da gwamnati ta fara zai amfani al’umma to dole mu kammala shi” cewar Lalong.
“Idan za ku lura a yanzu muna aiki ne a cikin sabon gidan gwamnati, kuma ba mu muka fara ginawa ba amma kuma ai mun kammala shi.”
“Zuwan mu karagar mulki mun kammala ayyuka da dama wadanda aka bari, kuma za mu ci gaba da yin su har saukar mu daga mulki, saboda gaskiya ni na tsani ganin ayyuka a yashe ba tare da an kammala ba”.
Gwamna Lalong da ya tabo bangaren ayyukan fannin kiwo lafiya da ilmi ya ce a yanzu yana da aniyar kammala sama da ayyuka arbain.