Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya amince da nadin Sen. Ibrahim Ida, a matsayin sabon shugaban jami’ar, Umaru Musa Yar’adua UMYU mallakin gwamnatin Katsina.
Abdullahi Yar’adua, daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Muntari Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Nada Injiniya Tukur A Matsayin Sabon MD Na NIGCOMSAT
“Nadin ya dogara ne da ikon da aka baiwa gwamna na tanadin jadawalin farko na kafa dokar Jami’ar mai lamba 7 ta shekarar 2006,” inji shi.
Mista Yar’adua ya ci gaba da cewa, an nada Ida ne bisa la’akari da irin kishin da yake da shi na yi wa bil’adama da gwamnati da jama’ar jihar hidima.
Ya ce: “Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa sabon shugaban jami’ar zai kawo kwarewarsa ta aiki da kuma dimbin gogewar da yake da shi a wannan sabon aiki domin ci gaban jami’ar baki daya.
“Masari ya yi amfani da damar don taya Ida murna tare da yi masa fatan Allah ya ba shi damar sauke nauyin da aka dora masa.”NAN
A wani labarin kuma,Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Halastaccen Dan Takarar Majalisa Na APC a Zamfara
Kotun daukaka kara dake zamanta a Sokoto a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, 2022, ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara ta yanke a watan Nuwamba, 2022, wanda ya tabbatar da nasarar Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Bungudu/Maru ta tarayya a jihar.
Wasu alkalai guda uku ne suka zartar da hukuncin; Alkalin kotun mai shari’a M L Shu’aibu, ya yi watsi da karar da Abdul Rahman Muhammad Tumbido ya shigar saboda rashin cancanta.