Kotun daukaka kara dake zamanta a Sokoto a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, 2022, ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara ta yanke a watan Nuwamba, 2022, wanda ya tabbatar da nasarar Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Bungudu/Maru ta tarayya a jihar.
Wasu alkalai guda uku ne suka zartar da hukuncin; Alkalin kotun mai shari’a M L Shu’aibu, ya yi watsi da karar da Abdul Rahman Muhammad Tumbido ya shigar saboda rashin cancanta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Manomi Ya Maka Kawar Matarsa A kotu Bisa Zarginta Da Sace Awakansa 4 A Kaduna
Ku tuna cewa mai shigar da kara Hon. Abdul Rahman Muhammad Tumbido ya garzaya kotun daukaka kara, yana kalubalantar hukuncin da wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Bappa Aliyu ta yanke ranar 27 ga watan Nuwamba 2022 a Gusau.
Wasu daga cikin rokon da mai shigar da kara ya yi sun hada da bukatar kotu ta bayyana zaben fidda gwanin da ya gabatar da Abdulmalik Zubairu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Bungudu/Maru a matsayin wanda ba shi da inganci, saboda saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da ka’idojin da jam’iyyar ta fitar a lokacin zaben fidda gwani.a matsayin dalilin tunkararsa zuwa kotu.
Tumbido ya kuma roki kotun da ta haramtawa wanda ake kara bayyana kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Bungudu/Maru da kuma bukatar ta umurci APC ta shirya tare da sake gudanar da zaben fidda gwani ga dan takararta.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, lauyan wanda ake kara, Barista P M Lasco Esq, ya ce hukuncin ya kore duk wani shakku kan takarar Hon.Abdulmalik Zubairu Bungudu a zaben fidda gwani.
“Lauyan ya kara da cewa, Hon Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu shine dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Bungudu/Maru a zaben 2023.
Da yake tsokaci kan hukuncin, wanda ake kara Hon. Abdulmalik Zubairu ya godewa Allah da ya ba shi nasara a karo na biyu, ya kuma yi kira ga mai kara da ya ajiye koke-kokensa na siyasa ya hada karfi da karfe domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Ya yabawa Gwamnan Jihar Bello Muhammad Matawalle; tsohon Gwamna, Hon. Abdul’aziz Abubakar Yari; Sanata Kabiru Garba Marafa da jiga-jigan magoya bayan jam’iyyar APC a mazabar tarayya da jiha baki daya domin nuna goyon baya da addu’oi.
A wani labarin kuma, Yadda Musulman New York Suke Cigaba da Kokawa kan rashin Binne Mamata
Lokacin da mahaifin Mohammad Abdullah ya yi rashin lafiya a shekarar da ta gabata, ya bayyana fata guda kawai. Bai so a kai gawarsa Pakistan don a binne shi ba. Ya so ya kwanta a New York, inda matar da ’ya’yan da zai bari a baya za su iya ziyarce shi cikin sauƙi. Don haka lokacin da ya rasu bayan wata guda, Abdullah ya tashi don ya cika burin mahaifinsa.
Amma bai kasance mai sauƙi ba.
New York tana da musulmai sama da miliyan ɗaya, amma babu makabarta na musulmi kaɗai. Akwai makabarta da ke samar da fili ga musulmi. Amma bayan barkewar cutar ta Covid-19, farashin filayen makabarta ya yi tashin gwauron zabo kuma ba a ba masallatai damar siyan filayen kaburbura kan farashi mai rahusa ba.