Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a ranar Laraba ya sanya hannu kan kasafin kudin 2021 zuwa doka, wanda ya kai naira biliyan 286.6.
Masari har wala yau ya jinjinawa ‘yan majalisar jihar bisa yadda suka yi saurin amincewa da kasafin kudin.
Ya tabbatarwa da al’ummar jihar Katsina cewa; gwamnatinsa za ta tabbata ta bunkasa walwalar jama’a, inda ya nemi goyon bayansu domin ci gaba jihar Katsina.