Lionel Messi ya ce, rashin rabuwarsa da Barcelona ya yi tasiri kan kwazonsa na taka leda a wannan kaka.
A cikin watan Agusta ne dan wasan na Argentina ya yi yunkurin amfani da wani sashi na dokar yarjejeniyarsa da Barcelona don raba gari da kungiyar a matsayin kyauta.
Sai dai Barcelona ta ki amincewa da yunkurinsa, tana mai cewa dole ne a ajiye Euro miliyan 700 kafin sakin dan wasan.
A yayin zantawarsa da gidan talabijin na La Sexta na Sifaniya, dan wasan ya ce, ya yi fama da abubuwa a farkon wannan kaka, amma a yanzu komai ya daidaita a cewarsa.