By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Edo, Kwamared Sunny Osayande ya rasu.
Jaridar Daily trust ta tattaro cewa ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi.
Sakataren NLC na Jihar Edo, Barry Imade, ya tabbatar wa wakilinmu rasuwar shugaban NLC na jihar.
Ya ce, “Eh, ya rasu jiya da daddare. Likitan zai gaya muku musabbabin mutuwarsa,” inji shi. Mutuwar Osayande na zuwa ne gabanin wani gangamin da ma’aikatan suka shirya yi a ranar 1 ga watan Fabrairu domin nuna adawa da karin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi ta’aziyyar rasuwar Osayande ga iyalansa.
Obaseki, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce jihar na cikin tsananin bakin cikin rashin babban abokin aiki kuma jigon kungiyar kwadagon Najeriya a jihar.