Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya amince da dakatar da wasu sarakunan gargajiya hudu a yankin Sankera Intermediate Area na jihar nan take, bisa zargin aikata madakalar da suka shafi kudi.
Wadanda aka dakatar su ne Mue Ter Ngyen, Cif D. K. Ijah daga Ukum; Mue Ter Ichongo, Cif Terngu Iorhuna; Mue Ter Ipusu, Cif Enoch Kyumen da hakimin Tir a karamar hukumar Katsina-Ala, Cif Boi Johnson.
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi da masarautu, Ken Achabo, a wata sanarwa da ya fitar ya nuna cewa, Tor Tiv, Farfesa James Ayatse, ya nada Cif Donald Vihive a matsayin Mue Ter Ngyen; Cif Stephen Tyôkpev a matsayin Mue Ter Ipusu, da Cif Orlu Mbakor a matsayin Mue Ter Chôngo.
Achabo ya kuma nuna cewa, Tor Sankera, Cif Abu King Shuluwa, ya kuma nada Cif Philip Saamaaya a matsayin hakimin riko na Tir.
Sai dai ba a bayyana tsawon lokacin da aka dakatar da kuma cikakkun bayanai kan zargin da ake yi wa Sarakunan da aka dakatar ba