Gwamnan jihar Nasarawa, Engr Abdullahi Sule, ya roki al’ummar Fulani da su amince da shirin bunkasa harkar kiwon dabbobi na gwamnatin tarayya (NLTP) wanda ake daf da farawa a jihar, domin wanzar da zaman lafiya tsakanin makiyayan jihar Nasarawa.
Ya yi wannan kiran ne a ranar ALhamis a garin Lafiya bayan da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar matasa Fulbe Ruga-Ruga da suka hada da maza da mata, a gidan gwamnatin jihar.
A cewar gwamnan, da shirin NLTP da ake shirin soma shi a jihar, musamman da kudurin gwamnatin tarayya na ware akalla Euro 400,000 daga gwamnatin Netherlands, domin tabbatar da shirin a jihar Nasarawa, al’umar Fulani za su amfana sosai ma damar suka karbi shirin hannu biyu biyu.
Gwamnan ya bayyana cewa gwmanatinsa ta aro wannan shiri na NLTP domin wanzar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma na jihar, yana mai cewa amincewar Fulani na shiga cikin shirin zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a jihar, la’akari da cewa za a karesu daga ‘yan bindiga da barayin shanu.
Ya yi nuni da cewa idan shirin ya fara, jihar Nasarawa ce ta farko a cikin jerin jihohin da su amfana da shirin na NLTP. Kuma za a samar da makarantu, sansanonin jami’an tsaro, wuraren yin kiwon dabbobi da shan ruwansu da dai sauran kayan bukatun Fulanin da dabbobinsu.
Da wannan gwamnan ya bukaci al’umar Fulani da su karbi shirin NLTP da hannu biyu biyu idan aka kaddamar da shirin a jihar.