Gwamnan jihar Ribas,Nyesom Wike ya nada Alhaji Abdulrazak Deprieye a matsayin babban mai gudanar da hukumar dake lura da aikin hajjin jihar. Wannan nadin ya fito a wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara akan kafafen watsa labaran rediyo da talabijin, Simeon Nwakaudu ya fitar.
Inda ya ce nadin ya fara aiki ne a nan take.
Gwamnan dai ya rushe shugabannin hukumar lura da aikin hajjin jihar ne ba tare da ya bayyana dalili ba.