Kungiyar SERAP ta nemi gwamnatin Afrika ta Kudu da ta biya diyyar Naira biliyan 10 na kashe baki da aka yi a kasarta ciki kuwa harda ‘yan Nijeriya. SERAP din ta nemi Soyata Maiga, shugabar kula da hukumar kare ‘yancin al’umma da ta kai kasar Afrika ta Kudu kotun kare hakkin dan Adam domin ganin an samar da hanyar da za a saukakawa ‘yan Nijeriya.
SERAP ta bayyana hakan ne a wata budaddiyar wasika da ta rubuta a ranar 6 ga watan Satumba, inda mataimakin Daraktan SERAP din, Kolawole Oluwadare ya bukaci hukumar da ta je kotun Afrika ta nemi a biya diyyar lalata dukiyoyi da rayuka ta hanyar biyan dala biliyan 10 a madadin daruruwa iyalai ‘yan Nijeirya.