Gwamna Wike ya yabawa Buhari kan sakin kason Neja Delta tun 1999
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da duk wasu kudaden da jihohin Neja Delta ke karba tun 1999.
Wike ya bayyana cewa, an yi amfani da wani bangare na kudaden ne wajen ayyuka da dama da gwamnatinsa ta gina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Sharia Ta Himmatu Wajen Inganta Shugabanci A Katsina
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin kaddamar da makarantar koyon aikin lauya ta Dakta Nabo Graham Douglas da gwamnatin jihar ta gina.
Ya yabawa shugaban kasa kan rashin wasa da kudin siyasa duk da kasancewarsa a wata jam’iyya ta daban.
A cewarsa, “Kudaden da ba a biya ba tun 1999, da aka cire kashi 13 cikin 100, Shugaban kasa ya amince kuma ya biya dukkan mu daga jihohin Neja Delta.
“A gare ni, ba zai zama rashin adalci ba a ce wa jama’a. Ba daga kudin FAAC ba ne, kudin da aka biya ni a matsayin Jihar Ribas, Jihar Delta, Jihar Akwa Ibom, Jihar Edo da Jihar Bayelsa.
“Don haka ina so da gaske, daga zuciyata da kuma a madadin gwamnati da jama’ar jihar, na gode wa Maigirma shugaban kasa kan hakan, domin a matsayinsa na gwamnatin adawa, yana iya cewa kada ku biya, ba za ku iya komai.
“Bayan haka tun 1999 ba a biya kudin ba. Shin mun yi wani abu?
“Don haka ina so in gode masa da gaske kan wannan
A wani labarin kuma: Dalilan daya sanya Peter Obi bazai samu ko Ƙuri’a ɗaya ba a Arewa
Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa, AYCF, ta ce jam’iyyar Labour Party, LP, da Ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ba za sy samu kuri’u ko kaɗan ba a Arewa.
Shugaban kungiyar AYCF na kasa, Yerima Shettima ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da za su raba kuri’u a yankin Arewa.