Gwamna Zulum ya taimaka wajan yakar ta’addanci a Lake Chad
Gwamanan Jahar Borno Umara Babagana Zulum ya baiwa kasar Tafkin Chadi taimakon motocin yaki goma don cigaba da aiki.
Abadam da Guzamala yanki ne da yayi kamari wajan ta’addanci a Kasar ta Tafkin Chad, kimanin mutane dubu uku da dari biyar sukai hijira zuwa Diffa da Bosso dake kasar Nijer.
Karanta:-Gwamna Matawalle ya Kori masu bashi shawara
Mazauna Diffa da Bosso sun sha alwashin zama da Yan gudun hijiran har na tsawon shekara bakwai saboda ganin tashin hankalin dake addabar yankin su.
Gwamna Zulum ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da Rundunar sojojin ta 68 a Malam Fatori.
In da yake cewa ” nazo nanne don in tattauna daku sannan na duba yadda za’a kawar da Yan ta’adda dake addabar yankin don dawowar Yan gudun hijira gida su”
Ya kuma umarci hukumar dake kula da samar da ruwa dasu gina famfuna a inda sojojin ke zaune.
Ya kuma ja hankalin sojoji kan bada kokarin don kawar da duk wani Dan ta’adda dake kai kawo a Malam Fatori, sannan gwamnan ya duba irin barna da Yan ta’adda sukayi a yankin.”
Ya kuma sha alwashin gyara duk wuraren da aka rusa cikin shekara daya, kamin ya gabatar da sojojin ya gana da shugan kasar Nijar Bazoum Muhammed a ranar Alhamis.
Yace a zaman, sun tattauna kan yadda za’a dawo da Yan gudun hijira zuwa gidajen su.
Yace zamu samar da kwamiti da zasu duba gine-gine don fara aiki cikin satinnan.
Tare da Gwamna Zulum akwai Abubakar Kyari Dan majalisa mai wakiltar Borno ta Yamma sannan da wasu wakilai daga Abadam da kuma Guzamala.