Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya sallami duk kannin manyan masu bashi shawara daga aikin su.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da sakataran gwamnati kuma Shugaban Ma’aikatan jihar, Alhaji Kabiru Balarabe ya fitar.
Balarabe ya ce, daga cikin wadanda aka sallama, ban-da Mai bai wa gwamnan shawara a kan harkokin tsaro, DIG Mamma Tsafe Mai ritaya.
Inda sanarwar ta ce” Hakan na sanar da al’uma cewa, Gwamna Matawalle ya sallami dukkannin masu rike da mukamin, masu bashi shawara, amma ban da Mai bai wa gwamnan shawara a kan harkokin tsaro.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar hadin guiwa ta kashe yan ISWAP
Balarabe ya kuma umarci dukkannin wadanda aka sallama da ga aiki, da su mika ragamar gudanar da aiyukan su, da dukkannin kaddarorin gwamnatin jihar, ga Babban Akanta na jihar Zamfara.
Ya kara da cewa, gwamnan jihar, ya yaba musu, bisa irin kokarin da sukayi na tabbatar da cigaban jihar Zamfara.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ta ruwaito cewa, ko a watan Fabbarairun shekaran nan, Gwamnan jihar Zamfara ya sallami dukkannin kwamishinonin jihar, masu bashi shawara, Manyan Daraktoci, daga aikin su, inda daga bisani ya maidawa wasu, da mukaman su a watan Afrilun shekarar 2021.
Idan za’a iya tunawa dai Gwamna Matawalle ya sanar da sauya sheka daga jam’iyar adawa ta PDP, zuwa Jam’iyar Mai Mulki ta APC a ranar 29 ga watan jiya, bayan kwashe watanni ana rade-radi zai yi hakan.