Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a daren ranar Litinin, ya bayyana a babban asibitin garin Bama a wata ziyar bazata, domin sa ido kan yadda ayyukan kiwon lafiya ke kaiwa ga jama’a.
Ziyarar ba-zatan da Zulum ya kai asibitin da misalin karfe 10 na dare jim kadan bayan isowarsa garin Bama ta hanyar Maiduguri, kokarin duba lokaci da jajircewar ma’aikatan lafiya wanda ya zama dabi’arsa na kai ziyarar ba-zata da daddare zuwa manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake fadin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kama Mutane 30 Da Ake Zargi Da Hannu A Wani Rikicin ‘Yan Kungiyar Asiri
Gwamnan ya kuma tafi makarantu da sassafe da kuma wasu lokutan domin lura da ingancin malamai da kuma ingancin koyarwa.
Yayin da Zulum yake asibiti ya yi murna da haduwa da ma’aikatan jinya da likitocin da ke bakin aiki.
Mista Olugbenga Aina shine wanda ya jagoranci gwamnan zuwa wajen zagayen cikin cibiyar kula da lafiya domin tantance aikin a kai a kai.
A wani labarin kuma, ‘Yan Fashi Sun Afkawa Wasu Bankuna Da Dama A Jihar Kogi
Wasu ‘yan fashi da makami sun kai farmaki a rassan bankunan UBA, Zenith da First Bank da ke Ankpa a jihar Kogi a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a tantance adadin su ba.
‘Yan fashin wadanda adadinsu ya kai 20, an ce sun shigo garin ne da misalin karfe biyu na rana. Da farko sun far wa bankin UBA, kafin su wuce zuwa bankin Zenith daga baya kuma suka afka zuwa FirstBank.