gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya bayyana yadda Asiwaju Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Lalong ya ce samu nasarar tasa ta biyo bayan mika mulki ga yankin Kudancin Najeriya da gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya na APC suka yi.
A cewarsa, an dauki matakin ne domin inganta hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya bisa tsarin adalci da daidaito…
DUBA WANNAN: Domin Samun Labarai
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya bayyana cewa nasarar da Asiwaju Bola Tinubu ya samu a matsayin zababben shugaban kasa ta biyo bayan mika mulki ga yankin Kudancin Najeriya da gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya na APC suka yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sake Zabar Wata ‘Yar Najeriya A Zaben Majalisar Birtaniya
Daily Post ta rawaito cewa Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Dakta Makut Simon Macham, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara shekara karo na 9 kan shugabanci na gari da aka gudanar a garin Lafia na jihar Nasarawa ranar Asabar.
A cewar sanarwar, an dauki matakin ne domin inganta hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya bisa tsarin adalci, daidaito wanda marigayi Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello ya tsaya a kai.
A cewarsa, Marigayi Sardauna ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali, hakuri, adalci da gaskiya, abin da ya gada ya dawwama bayan rasuwarsa kuma yana ci gaba da zaburar da shugabanci a yankin da kasa baki daya.
Sanarwar ta kuma bukaci daukacin ‘yan Nijeriya na yankin Arewa da ma fadin kasar nan da su marawa zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya a yayin da yake rike da ragamar shugabancin kasar.
Inda ya kara da cewa Arewa muhimmiyar mai ruwa da tsaki ce a harkokin Nijeriya da irin gudunmawar da ta ke bayarwa ga shi. ba za a iya kara jaddada zaben ba.
“Lokacin da na jagoranci takwarorina Gwamnonin Arewa na APC suka tura mulki zuwa kudu, ba wai don muna son Asiwaju ya zama Shugaban kasa ba.
“A maimakon haka, muna son tabbatar da adalci da gaskiya a cikin al’ummarmu domin hadin kai da zaman lafiya da lumana.
“Wannan shi ne abin da muka yi imani da cewa mahaifinmu mai albarka Sir Ahmadu Bello zai yi a irin wannan yanayi. An yi sa’a, wakilan jam’iyyar sun zabi Asiwaju wanda a karshe ‘yan Najeriya suka karbe shi domin an zabe shi gaba daya”. Inji Lalong
Ya ce yankin Arewa na bukatar kulawa sosai a sassa daban-daban da suka hada da tsaro, ilimi, samar da ababen more rayuwa, noma, farfado da tattalin arziki da kuma maido da doka da oda a fannoni daban-daban da rashin tsaro ya daidaita.
Ya ce kungiyar gwamnonin Arewa a karkashin shugabancinsa sun yi ayyuka da yawa wajen hada kan jama’a a matsayin masu makoma guda daya.
A wani labarin kuma, IG Ya Sake Tura Wasu Manyan Jami’an ‘Yan sanda 86 da ACPs 206
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya bayar da umarnin sake tura wasu manayan jami’an ‘yan sanda wurare daban-daban.
Manyan jami’an da aka tura sun hadar da manyan kwamishinonin ‘yan sanda 86 da ACPs 206.