Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya bayar da umarnin sake tura wasu manayan jami’an ‘yan sanda wurare daban-daban.
Manyan jami’an da aka tura sun hadar da manyan kwamishinonin ‘yan sanda 86 da ACPs 206.
Sake tura jami’an shine don kawar da masu aikata munanan laifuka tare da inganta harkokin tsaron cikin gida…
DUBA WANNAN: Domin Samun Labarai
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, ya bayar da umarnin sake tura mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 86 da ACPs 206 a sassan shiyyoyin ‘yan sanda da na jihohi a fadin kasar nan,Punch ta rawaito.
Manyan jami’an ‘yan sanda sune wadanda za su nada sauran manyan kwamishinonin ‘yan sanda da sauran manyan jami’ai wajen gudanar da muhimman ayyuka na gudanarwa, bincike don ingantaccen tsarin aikin ‘yan sanda a fadin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jarabawar UTME: An Samu Ƙarancin Rashin Cin Zarafi A Bana
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a ranar Asabar a wata sanarwa da wakilinmu ya samu.
Adejobi ya ce, “An yi wannan turawar ne domin karfafawa da kuma inganta hanyoyin tsaron kasa wajen samun ingantaccen tsarin ‘yan sanda a fadin kasar nan.
“IGP ya baiwa jama’a tabbacin gudanar da zage damtse a kowane fanni domin tabbatar da ‘yan sandan Najeriya yadda ya kamata da kuma karfafa tsaron cikin gida kamar yadda aka umurce su da kuma yin kira da suyi aiki domin ci gaban kasarmu.
“Ya umarci manyan jami’an da su tabbatar da dabarun nuna kwarewa, sadaukar da kai ga hidima, mutunta hakki, da samar da ingantattun dabaru don dakile laifuka.
“Kazalika ya bukace su da su cimma nasarar manufofin rundunar, mafi girman matakin kwarewa, aikin jama’a na al’umma, da bin bin doka.”
Adejobi ya kuma kara da cewa Baba ya nanata kudurin shugabancin hukumar ta NPF na inganta ayyukan ‘yan sanda a dukkan fannoni domin cimma manufofin aikin ‘yan sanda na zamani, inda ya kara da cewa ta himmatu wajen ci gaba da gudanar da ayyukan inganta harkokin tsaron cikin gida a Najeriya.
A wani labarin kuma, Jam’iyyar Labour Party Ta Dakatar da Wasu Mambobinta Uku
Jam’iyyar Labour Party reshen Jihar Kaduna, ta dakatar da wasu mambobinta guda uku masu dauke da katin jam’iyyar da suka halarci “ taron data kira “Taron kwamitin zartarwa na kasa NEC” da ya gudana a jihar Bauchi a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu, 2023.
Daga cikin wadanda aka dakatar sun hada Bashir Idris Aliyu da Alhaji Ibrahim Sidi Bamali da Injiniya Michael Ayuba Auta kuma za a mika hukuncin dakatar da su ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Labour na kasa da sauran hukumomin da abin ya shafa domin daukar mataki