By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Abdulkadir Mohammed, CON kauran Bauchi, ya amince da dakatar da shugaban zartarwa na hukumar marayu da marasa galihu ta jihar Bauchi (BASOVCA) Misis Hassana Arkila.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai bada shawara na musamman kan harkokin yada labaran gwamna, Mukhtar Gidado ya fitar a ranar Litinin.
Yace Umurnin dakatarwa wanda ya fara aiki nan take shi ne a bada damar gudanar da bincike na gaskiya kan al’amuran Hukumar biyo bayan zargin rashin da’a.
Sakamakon haka, an bukaceta data mika lamuran hukumar ga babban jami’in kungiyar har zuwa lokacin da gwamnati za ta kammala gudanar da bincike.
Comments 1