By Ishaq Dabai
Wani matashi mai suna Samson Odunayo tare da abokan aikinsa guda biyu sun shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun bisa zargin su da laifin yi wa wani mai babur din dan kasuwa Bashiru Umaru kisan gilla kafin ya sace babur dinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa cewa Odunayo, dan shekara 18, ya furta aikata laifin daya aikata saboda yana bukatar kudi Naira 500 a wajen sa don ya sayi datar shiga yanar gizo.
Odunayo wanda aka kama tare da wasu matasa biyu, Sodiq Awokoya da Jimoh Rilwan a ranar Juma’a, a yankin Ogere na jihar, an gabatar dasu gaban manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Eleweran, Abeokuta, babban birnin jihar.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, yace an kama matasan ne yayin da suke kokarin sayar da babur din.
Da yake magana da manema labarai, Odunayo wanda shi ma yace shi dan damfara ne ta kafar sadarwar intanet, yace ya aikata laifin ne saboda yana cikin bukatar kudi cikin gaggawa don siyan datar shiga shafin sadarwa don yin rajista.
Kazalika yace,“Sodiq ne ya jawo ni cikin ayyukan masu laifi.Shi ne aikinmu na biyu kafin a kama mu. Aiki na farko da muka gudanar, ba mu kashe wanda abin ya shafa ba, kawai mun karbi kudi Naira 3,500 daga gare shi.
“Na yarda na fara aikin domin in sami kudi sayan datar shiga yanar gizo dan in yi rajista da intanet don gudanar da hakar damfara ta yanar gizo wacce akafi sani da (yahoo), Ban kashe kowa ba a da.”in jishi