Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya gwangwaje alhazan jihar da tsabar kudi Riyal 300 ga kowanne mahajjacin Bauchi su fiye da 3,000 a kasa mai tsarki ta Makkah.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Alhaji Mukthar Gidado ya fitar ranar Juma’a a Bauchi.
KARANTA WANNAN: Na Karanta Al-Qur’ani Ya Sa Ni Kuka – Budurwar Dan Wasa Benzema Ta Musulunta
Gidado ya ce gwamnan ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci sansanin Bauchi da ke kasa mai tsarki domin mu’amala da mahajjata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Riyal 300 na kasar Saudiyya ya yi daidai da Naira N75,000.
Gidado ya ce gwamnan ya yi hakan ne domin yaba wa alhazai kudaden da suka kashe a lokacin zamansu a kasa mai tsarki.
Ya ce gwamnan, a ziyarar da ya kai tantin alhazan da ke Minna, ya yaba da yadda suka nuna kyakykyawar dabi’ar da suke yi a kasar Saudiyya.
“Mohammed ya yaba musu bisa mutunta hukumomi, a Najeriya da kuma a kasar Saudiyya.
“Ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa hukumar jin dadin alhazai ta jiha domin samar da ayyuka masu inganci ga alhazai,” inji shi.
Gidado ya kuma ce gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da hukumar alhazai ta kasa NAHCON don magance wasu kalubalen da hukumar alhazai ta jihar ke fuskanta a filin ajiye motoci.
Ya ce gwamnan ya nuna matukar godiyarsa ga maniyyatan bisa addu’o’in da suke yi na samun nasarar gwamnatin sa, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin. NAN
A wani labarin kuma,Cikakken Jerin Jihohin da Suka Samu Sabbin Kwamishinonin ‘Yan Sanda
Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda.
DAILY POST ta rahoto cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan shine Alamatu Abiodun Mustapha.