Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya nada Mista Chooks Oko a matsayin sabon mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru.
Oko ya kasance har zuwa nadin nasaanasa a matsayin mataimaki na musamman ga gwamnan kan dabarun.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-yan-bindiga-sun-kai-hari-ofishin-yan-sanda-sun-hallaka-wani-jamii-a-jihar-ondo/
An bayyana nadin ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Ugbala Kenneth Igwe, ya fitar ranar Lahadi.
Sabon maitaimaka wa kan kafafen yada labarai ya maye gurbin tsohon mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Francis Nwaze.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa nadin Oko a matsayin mai magana da yawun gwamnan shi ne na biyar tun bayan da Umahi ya zama Gwamna a shekarar 2015.
Ugbala ya ce Gwamnan ya sake nada tsohon maitaimaka masa kan harkokin yada labarai a matsayin mataimaki na musamman kan takardu.
Ya ce, “Mai girma Gwamnan Jihar Ebonyi, Engr. Cif David Nweze Umahi ya amince da sake nada SA na Gwamna akan harkokin yada labarai, Deacon Francis Nwaze a matsayin SA akan takardu yayin da SA na Gwamna akan Dabaru, Mista Chooks Oko ya zama SA kan kafafen yada labarai da dabaru.
“Bisa la’akari da abubuwan da ke sama, mikawa da karbar ayyuka na nan take. Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda abin ya shafa su tabbatar da bin wannan umarnin.
A Wani Labarin Kuma Fadar shugaban kasa ta sanar da nadin Honorabul Nasiru Baballe Ila a matsayin sabon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar wakilai ta kasa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ya sanya wa hannu, ta ce Buhari ya amince da nadin Hon Nasiru, wanda ya fito ne daga kwalejin Victory ta Alexandria da West London College da ke kasar Ingila.
Fadar shugaban kasa ta bayyana Nasiru a matsayin hamshakin dan kasuwa mai sha’awar sha’anin safarar kaya da sana’ar fata kafin ya shiga harkokin siyasa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a shekarar 2011 zuwa 2015, an zabi Nasiru a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni a Kano.
Yanzu ya maye gurbin Hon.Umar Ibrahim El-Yakub wanda shugaban kasa ya nada minista.