Gwamnan jihar Filato Barista Simon Bako Lalong, ya mika wa majalisar dokoki ta jihar sunayen mutanen 23 da yake so ya nada su kwammishinoni don tantancewa.
Kakakin Majalisar, Honarabul Abok Izam, ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar da aka gabatar a ranar Talatar nan da ta gabata.
Shugaban majalisar ya ce akwai tsoffin kwamishinoni biyar daga cikin jerin sunayen kwamishinonin da Gwamnan ya tura wa majalisar, inda ya karanta sunayensu kamar haka: bictor Lapbag, Elizabeth Wapmuk, Yakubu Datti, Tapgun Sylbanus Dankano, Barista Chrisantus Ahmad, Ibrahim Sa’ad Bello da Barista Rimben Bitrus Zulfa.
Daga cikin sunayen har wala yau akwai: Nimkom Lar Ndam, Alhaji Dayyabu Garga, Hosea Istifanus Finangwai, Tamwakat Weli, Regina Soemlar, Kak’mena Goteng Audu, Usman Yakubu Idi da Dakur Jude Eli.
Honarabul Izam, ya kara da cewa sauran su ne: Dan Manjang, Muhammad Muhammad Abubakar, Sylbester Wallangko, Dung Musa Gyang, Pam Botmang, Jerry Were, Sambo Rabecca Adar da Abe Aku.
Shugaban majalisar, ya tabbatar wa Gwamnan cewa a cikin ‘yan kwanaki kalilan majalisar za ta kamala tantance sunayen ta mika masa don ya sa hannu domin rantsar da su su fara aiki.
Leadership A Yau sun tabbatar da cewa; Honarabul Izam, ya yi amfani da wannan daman wajen yin kira ga al’ummar jihar da su kara bai wa gwamnan goyon baya don ya sami kwarin guiwar aiwatar da dimbin ayyukan da ke gabansa.