Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya nada Salihu Baba Alkali a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta Gombe GIRS.
Bayanan hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ismaila Uba Misilli ya fitar ta ce nadin wanda ya fara aiki nan take sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya mika shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Nemi ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Su Dakatar Da Kamfen Nasu Kan Wani Dalili
A jiya Alhamis ne dai Gwamnan ya nada Salihu Baba Alkali a wannan mukamin na sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar.
Wanda aka nada,ya kasance kwararre ne kan harkokin kudi da haraji, ya yi ritaya kwanan nan a matsayin darekta daga Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya FIRS.
A wani labarin kuma, Ma’aikata sun rufe Sakatariyar Plateau kan rashin biyan Albashi
Ma’aikatan karamar hukumar Lantang ta Arewa da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun rufe sakatariyar karamar hukumar.
Wasu daga cikin fusatattun ma’aikatan da suka zanta da jaridar PUNCH a Jos, sun ce sun yanke shawarar rufe sakatariyar ne domin yin rajistar kokensu kan rashin biyansu albashi sama da watanni hudu.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan da ta ki bayyana sunanta ta ce, “da sanyin safiyar yau (Alhamis), ma’aikatan karamar hukumar Langtang ta Arewa da dama sun gudanar da zanga-zangar lumana domin yin rajistar kokensu na rashin biyansu albashin watanni shida da karamar hukumar ta yi.