By Abbas Yakubu Yaura
A kokarin sa na zamanantarwa da saukaka harkar yada labarai na gidan Talabijin, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon tsari da aka fi sani da (DSO) a Jihar Kano.
Sabon tsarin da aka yiwa lakabi da (DSO) Manufar sa itace yin kaura daga tsohon tsarin yada labaru izuwa ga sabon tsarin yada labarai na zamani.
An kaddamar da shirin ne karkashin Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta kasa (NBC) a dakin taro na Coronation Hall dake gidan Gwamnatin Jihar Kano.
A jawabin sa, ministan yada labarai na kasa, Alhaji Lai Muhammed wanda ya kasance babban bako a wurin taron, ya yabawa Gwamnan bisa hadin kai da dukkannin goyon baya daya bayar wajen ganin an kaddamar da sabon tsarin a Kano.
A jawabin Gwamnan, yace tsarin yayi daidai da zamani kuma zai taimaka mutuka wajen bunkasawa tare da saukaka harkar yada labarai da kuma saukaka kashe kudin sabuntawa ga masu amfani manhajar.
Sannan ya kara da cewa gwamnatin sa zata kara bada goyan baya wajen ganin tsarin ya dore dan kirkiro ayyuka da samar da damamarmaki ga matasa da kuma kawo cigaba a daidai lokacin da tuni an riga an horas da wasu matasan akan yadda zasu rika hadawa da kuma sarrafa manhajar ga masu amfani da ita.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Daga cikin mahalarta taron sun hada da Mataimakin Gwamnan, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed sai kwamishinan yada labarai, kwamared Muhammad Garba da shugabar gidan talabijin na ARTV Hajiya Sa’a Ibrahim da kuma Shugan Hukumar (NBC) Balarabe Ilelah da sauran shugannin Hukumomin yada labarai na kasa da sauran manyan mutane da manyan jami’an Gwamnati.
Comments 1