Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Danko Wasagu da ke jihar kan hare-haren ‘yan bindiga da suka yi sanadin mutuwar mutane goma sha uku da suka hada da sojoji biyu da dan sanda daya.
Al’ummomin sun hada da, Ragan, Morai, Warkata, Wadaku, Dankade, Yar-Kuka, Gaya, Ayu da Unashi.
Bagudu ya kuma yi jawabi ga ‘yan gudun hijirar da ke makarantar firamare ta Nizzamiya da ke garin Waje a Danko Wasagu kan hare-haren wuce gona da iri.
Gwamna Bagudu ya bayyana cewa ya je yankin ne domin jajantawa al’ummar jihar da gwamnatin jihar, tare da yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa iyalan wadanda suka rasu karfin gwuiwa wajen daukar hakurin jure rashi.
Ya ce ana kan kokarin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro na ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Gwamna Bagudu ya amince da irin namijin kokarin da jami’an tsaro, malaman gargajiya da na addini, da kuma ‘yan banga suka yi a kan haka.
Ya ce gwamnatin jihar ta saba baiwa jami’an tsaro motoci da sauran kayan aiki, domin tallafa musu a harkokinsu.
Ya ce kalubalen tsaro ya barke ne daga jihar Zamfara mai makwabtaka da jihar kuma gwamnatin jihar Kebbi tana hada gwiwa da makwabtanta domin magance munanan dabi’u.
Gwamnan ya roki al’ummar jihar da su kara hakuri da imani da addu’o’i da jajircewa, duk da cewa gwamnati za ta biya wa ‘yan gudun hijiran bukatun rayuwa.
Ya kuma yi gargadi game da yada labaran karya da sauran labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta wadanda a cewar sa za su kara dagula al’umma.
Gwamnan ya samu rakiyar Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu Sanata Bala Ibn Nallah da wasu manyan jami’an gwamnati.