Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan janye sojojin Najeriya daga cibiyoyin da suka yi na gyaran hali a fadin jihar.
Ya zargi Sojoji da daukar matakai na karya gidan yari.
Gwamna Akeredolu, wanda ya samu cikakken bayanin halin da ake ciki daga kwamishinan ‘yan sanda, Oyediran Oyeyemi, ya damu cewa matakin zai iya karfafa fasa gidan yari.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde, gwamna Akeredolu ya yi mamakin dalilin da zai sa za a janye sojoji daga cibiyoyin gidan gyaran hali na gwamnatin tarayya.
“A daren jiya, Gwamna Akeredolu ya samu rahoto daga kwamishinan ‘yan sanda a jihar cewa an janye sojojin da ke tsare cibiyoyin gidan gyaran hali a jihar.
“Wannan al’amari ya zo da mamaki, duba da yadda rundunar sojojin Nijeriya da kuma cibiyoyin gyaran hali na gwamnatin tarayya suke.
“Gwamnan ya fi damun sa game da illar ambaliya da janyewar sojoji ke yi a harkar tsaro a jihar. Kari ta yadda irin wannan matakin zai iya kwadaitar da fasa gidajen yari cikin sauki a fadin jihar.
“Duk da haka, ya dace a fadakar da jama’a da gwamnatin tarayya kan wannan yanayi mara kyau. Binciken da aka yi kan musabbabin wannan aikin ya nuna cewa umarni ne daga sama ba tare da cikakkun bayanai ba.
“Abin da ya ki ci ya ki cinyewa, an yi namijin kokari wajen ganin an tabbatar da tsaron wadannan cibiyoyi domin kada a bari a fasa gidajen yari da aka tsara domin duk wanda ya ba da umarnin janye wadannan sojoji yana kan ci gaba da karfafa irin wannan.” Sanarwar ta kara da cewa.
Gwamna Akeredolu ya gana da wasu shuwagabannin tsaro a jihar, musamman ‘yan sanda, inda ya umarce su da su karbi aikinsu na tsaron cikin gida a jihar.
“Duk da cewa mun yi imanin cewa ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta kare gidajen yari, amma mun fi damuwa da tsaron al’ummarmu a fadin jihar nan. Fasa gidan yari ba wai kawai zai kawo barazana ga zaman lafiya da muke samu a jihar ba, zai haifar da babbar hatsari ga al’ummar mu.
“Gwamna Akeredolu ya gana da shuwagabannin tsaro, kuma tun a daren jiya ‘yan sanda suka dauki nauyinsu na tsaron cikin gida ta hanyar tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa wadannan cibiyoyin gida gyara haki.
“Hakazalika, hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) wacce babban aikinta shi ne tabbatar da tsaro a cibiyoyin gwamnatin tarayya, ta kuma tura jami’anta masu dauke da makamai zuwa wuraren gyaran halin.
“Gwamna Akeredolu ya kuma bayar da umarnin tura jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (Amotekun) domin su taimaka wa ‘yan sanda da NSCDC. Wannan shi ne don tabbatar da cewa duk wani aiki da aka tsara an datse shi kuma an hana shi da karfin da ya dace.” Sanarwar ta kara da cewa.