Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace nan bada jimawa ba zai mikawa majalisar dokokin jihar Kano sunayen sabbin kwamishinoni domin tantancewa.
Ganduje ya ce zai miƙawa majalisar sunayen sabbin kwamishinonin ne domin maye gurbin tsaffin kwamishinonin da suka samu takara a matakai daban-daban a jam’iyyar APC.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar zartaswar na mako-mako, wanda aka gudanar a zauren taron Majalisar dake gidan gwamnatin Kano.
DUBA WANNAN LABARIN: ASUU ta bukaci Dalibai su kara hakuri da matakin da ta dauka
” Kamar yadda kuka sani akwai wasu daga cikin ƴan wannan majalisar da suka sami takara a jam’iyyar APC, don haka dole mu maye gurabensu da sabbi don cigaban jihar Kano “. Inji Ganduje
Kimanin kwamishinonin 8 ne suka ajiye aikinsu domin yin takara a jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa na 2023.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa daga cikin Kwamishinonin da suka ajiye aikinsu, akwai Sadiq Walid wanda yanzu haka shine ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar.